Ministan wasanni da al'amurran matsa na kasar Morocco, Rachid Talbi Alami, da takwaransa na Ivory coast, Francois Albert Amichia, sune suka jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar ta tsawon shekaru 5, wanda aka kullata da nufin karfafa mu'amala ta fuskar bada horo da kuma kyautata alaka a fagen wasanni tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu, zasu dinga yin musayar kwarewa da musayar bayanai a sha'anin gudanar da al'amurran wasanni da samar da kayayyakin wasanni, da magungunan da suka shafi wasanni, da kuma yaki da matsalar yin zamba da tada husuma a filayen wasanni.(Ahmad Fagam)