180118-mene-ne-wasan-kwallon-zilliya-bello.m4a
|
A lokacin da ake son gudanar da wasan kwallon zilliya, a kan jera kwallaye a kan layin dake tsakiyar filin wasan, sa'an nan 'yan wasa za su yi gudu zuwa tsakiyar fili domin daukar kwallayen da aka jera a tsakiyar sa. Bayan da aka samu kwallo a hannu, ba a yarda a jefa wa abokan karawa nan take ba, sai bayan an mika ta ga wanda ake kungiya daya da shi, daga bisani za a iya kai hari da kwallon.
Idan kwallon da aka jefa ya taba bangaren jikin wani kai tsaye, wato kafin kwallon ya taba jikin mutum bai taba dabe ko kuma bango ba, kuma bayan da ya taba jikin mutum ba wanda ya tare kwallon kafin ya fadi kasa, to, dan wasan da kwallon ya taba jikinsa ya fita, ba zai ci gaba da kasancewa cikin filin ba ke nan, zai koma wani wuri na musamman da aka kebe ya tsaya a can. Duk wanda ya nemi tare kwallon da aka jefa masa, amma kwallon ya fadi daga hannunsa, to, shi ma zai koma wajen filin wasa, wato ba a yarda ya ci gaba da wasa.
A daura da haka, idan wani ya karbi kwallon da aka jefa masa, wato ya samu damar tare kwallon da hannunsa kafin ya ci karo da jikinsa, to, hakan zai nuna cewa dan wasan da ya jefa kwallon bai yi nasara ba, don haka wannan dan wasa zai tafi wajen filin wasa. Sai dai a nan ana bukatar wanda ya karbi kwallon ya rike shi a hannu har tsawon dakika 2, kafin daga bisani a kori dan wasan da ya jefe shi da ita daga cikin fili.
Idan kwallon da aka jefa ya taba jikin wani dan wasa, amma daga bisani wani abokinsa ya cafke ta da hannu kafin ya fadi kasa, to, hakan zai sa a kori dan wasan da ya jefo kwallon, kuma za a ba wanda ya karbi kwallon damar dawo da wani abokin wasansa cikin fili, wanda ke jira a wurin da aka kebe, cikin filin wasa. Ban da haka kuma, wanda kwallon ya taba jikinsa a wannan karo ba zai bar filin wasan ba.(Bello Wang)