in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan Triathlon da ya kunshi wasanni uku
2017-12-29 06:37:26 cri


An ce an fara gudanar da wasan Triathlon ne a shekarun 1920 a kasar Faransa, inda aka fara kiran wasan da sunaye daban daban, irinsu "wasanni 3", "wasa na masu kwarewa", da dai sauransu. Sai dai akwai bayanin da ya nuna cewa, tun daga shekarar 1902, an riga an fara gudanar da wani wasa na musamman da ya hada wasan tseren gudu a kafa, da na kekuna, gami da tseren kwale-kwale a waje guda.

A shekarar 1920, wata jaridar kasar Faransa mai taken L'Auto ta watsa wani labari dake cewa, an gudanar da wata gasar da ake kira "wasa na 3", inda mahalarta gasar suka yi tseren gudu na tsawon kilomita 3, da tseren kekuna na tsawon kilomita 12, gami da ketare wani mashigin teku da ake kira "Marne" ta hanyar ninkaya. Wajen waccan gasar, an gudanar da wasannin 3 bi da bi, ba tare da tsayawa tsakaninsu ba.

Sa'an nan zuwa shekarar 1921, a birnin Marseilles na kasar Faransa, an gudanar da wata gasar da ta yi kama da waccan na baya, inda aka fara da wasan tseren keke, sa'an nan an yi tseren gudu, kafin an yi wasan ninkaya a karshe.

Sa'an nan gasar da ta kunshi wasannin ninkaya, da tseren keke, da kuma tseren gudu, wanda aka fara kiranta "Triathlon" a karon farko, ita ce wata gasar da aka gudanar a birnin San Diego na kasar Amurka, a shekarar 1974. 'Yan Amurka 2 Jack Johnstone da Don Shanahan ne suka tsara wannan gasa, wadda ta samu 'yan wasa 46 da suka halarce ta.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China