in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan kasar Masar Mohamed Salah ya zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na Afirka a shekarar 2017
2018-01-10 16:06:21 cri

A ranar 4 ga wata ne hukumar wasan kwallon kafa ta Afirka ta sanar a birnin Accra na kasar Ghana cewa, dan wasan kasar Masar Mohamed Salah wanda ke wasa a kungiyar Liverpoor ta kasar Ingila, ya zama dan wasan kwallon kafa mafi kwarewa na nahiyar Afirka na shekarar 2017.

Salah mai shekaru 25 da haihuwa ya doke dan wasan kasar Senegal Sadio Mané da kuma dan wasan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang inda ya lashe wannan kambu.

A jawabinsa Salah ya bayyana cewa, ya cimma burinsa, shekarar 2017 shekara ce mai muhimmanci a gare shi, kana ya yi farin ciki sosai kan yadda kasarsa ta Masar ta samu nasarar shiga gasar cin kofin kwallon kafan duniya na shekarar 2018 da za a buga a Rasha. Dan wasan ya taka rawa a yayin da yake taka leda a kungiyar Rome ta kasar Italiya da kuma kungiyarsa ta yanzu ta Liverpoor ta kasar Ingila. Salah ya kuma nuna godiya ga iyalansa saboda goyon bayan da suka nuna masa, kana yana alfahari da samun wannan lambar yabo.

Ya zuwa yanzu a wannan kaka, Salah, dan wasan kungiyar Liverpool ya ya ciwa kungiyar sa kwallaye 17, kuma shi na biyu wajen yawan cin kwallo a yanzu a gasar Premier ta Ingila. Ya taimakawa kungiyar ta Liverpool sake shiga rukunin kungiyoyi 16 da ke buga gasar zakarun Turai bayan shekaru 9.

Salah, ya taimakawa kasar Masar, samun damar shiga gasar cin kofin kwalllon kafan duniya da za a buga a Rasha, wanda rabonta da samun wannan dama tun shekaru 28 da suka gabata. Masu sha'awar kwallon kafa a kasar Masar na kallon sa a matsayin tauraron kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China