in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambia: An kaddamar da shirin raya kasa na shekaru 4
2018-02-07 10:44:06 cri

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow, ya kaddamar da wani sabon shirin raya kasa wanda za a aiwatar a cikin shekaru 4 masu zuwa.

Shirin wanda aka kaddamar a ranar Talata, na kunshe da cikakkun manufofin gwamnatin kasar da na abokan huldar ta masu fatan tallafawa ci gaban ta, kamar dai yadda shugaba Barrow ya bayyana.

Tun daga shekarar nan ta 2018 za a fara aiwatar da sabbin manufofin, wadanda za su samar da managarcin tsarin aikin gwamnati, da gudanar da al'amura a fayyace, da inganta zamantakewar al'umma, tare da aiwatar da matakan hadin kan 'yan kasar.

Wannan ne dai karon farko da sabuwar gwamnatin kasar ta fidda irin wannan tsari na samar da ci gaba, tun bayan da shugaba Barrow ya kama aiki a matsayin jagoran kasar shekara guda da ta gabata.

Mr. Barrow dai ya zargi tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, da laifin karya ka'idojin aikin hukuma, wanda hakan ya haifar da tsundumar kasar dake yammacin Afirka cikin bashi da yawan sa ya kai dalar Amurka biliyan daya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China