in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tura sojoji zuwa kasar Gambia
2017-01-19 10:00:16 cri

A jiya Laraba ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da tura sojoji da jiragen saman yaki zuwa kasar Gambia, a wani mataki na kara karfin dakarun kungiyar kasashen ECOWAS na ganin an martaba sakamakon zaben shugabancin kasar na ranar 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata.

Kakakin sojojin sama na Najeriya Ayodele Famuyiwa ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai cewa, sojojin da za su aiki a kasar ta Gambia, za su tashi ne daga rukunin sansanin samun horon mayakan kasar na Kainji da ke jihar Neja. Kuma za su yada zango ne a Dakar, babbar birnin kasar Senegal.

Wannan tawaga dai ta kunshi dakaru na musamman da jami'in lafiya da kuma masu aikin injiniya. Bugu da kari, Najeriyar ta tura jiragen saman yaki, da jiragen yaki masu saukar ungulu da sauransu.

Kungiyar tarayyar Afirka AU da kungiyar ECOWAS suna shirin kawar da shugaba Yahya Jammeh daga mulki da karfin tuwo, tare da rantsar da mutumin da 'yan kasar suka zaba Adama Barrow.

Shi dai shugaba Jammeh ya ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 1 ga watan Disamban shekarar da ta gabata ce, bayan da tun farko ya amince da kayen da ya sha a hannun Adama Barrow.

A yau Alhamis ne dai ya kamata a rantsar da Adama Barrow, wanda yanzu haka ya arce zuwa kasar Senegal don gudun barkewar tashin hankali.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China