in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar shugaban Gambia ta ce ba wani abun damuwa game da batun tsaron kasa
2017-07-14 10:04:59 cri

Daraktar watsa labarai ta shugaban kasar Gambia Amie Bojang-Sissoho, ta bukaci daukacin al'ummar kasar da su kwantar da hankulan su, su kuma yi watsi da rade radin da ake yi cewa, wasu dakaru daga tsallaken iyakar kasar na shirin kaiwa kasar farmaki.

Amie Bojang-Sissoho ta ce, shugaban kasar Adama Barrow na sane da wannan lamari, sai dai kuma ya yi amannar cewa, duk wasu dakaru da za su kaiwa kasar hari, za su yi hakan ne ta kan iyakokin ta na kasa ko na ruwa, kuma jami'an tsaron kasar na cikin shirin ko ta kwana, domin dakile duk wata barazana mai nasaba da hakan.

Jami'ar wadda ta yi wannan tsokaci yayin taron manema labarai da ya gudana jiya Alhamis a Fajara ta kara da cewa, dakarun tsaron Gambia na hadin gwiwa da na kasashe makwafta domin tabbatar da tsaron kasar.

A farkon makon nan ne dai aka fara yayata jita-jitar cewa, sojojin dake biyayya ga tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, na shirin aukawa kasar daga wani sansanin su dake wajen kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China