in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Gambia sun amince su zurfafa musayar bayanai ta fuskar ayyukan majalisun dokoki
2017-09-19 08:55:14 cri

Kasashen Sin da Gambia sun amince su zurfafa hadin gwiwa da musayar bayanai dangane da ayyukan da suka shafi majalisun dokoki.

An cimma wannan ne a jiya Litinin, lokacin da babban jami'in majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin NPC Zhang Dejiang, ya gana da shugabar majalisar dokokin Gambia Mariam Jack Denton a nan birnin Beijing.

Zhang Dejiang wanda shi ne shugaban kwamitin gudanarwa na majalisar NPC, ya ce sake kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu wani sabon babi ne na kara aminta da juna a fannin siyasa da hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya, tare da inganta hulda tsakanin al'ummomi.

Ya ce, kasar Sin na daukar dangantakarta da Gambia da muhimmanci, kuma tana goyon bayan sabuwar gwamnatin kasar, a kokarin da take na inganta rayuwar jama'a da samar da ci gaba mai dorewa.

Zhang Dejiang ya kuma yi kira ga bangarorin biyu su mara baya ga juna kan muhimman batutuwa da suka shafe su.

A nata bangaren Mariam Denton cewa ta yi, Gambia ta dauki dangantakarta da kasar Sin da daraja, kuma ta yi amana da manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Ta ce, a shirye majalisar dokokin Gambia take, ta kara ganawa da majalisar NPC ta kasar Sin, tana mai bayyana fatan kara inganta hadin gwiwa da kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China