in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gambia tana shirin komawa kungiyar kasashe renon ingila da ICC
2017-06-23 11:04:32 cri

Nan ba da dadewa ba kasar Gambia za ta sake zama mambar kungiyar kasashe renon Ingila da na kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ICC, biyo bayan matakin da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya dauka a baya na janye kasar daga wannan kungiya.

Darektar watsa labarai da hulda da jama'a ta fadar shugaban kasar Amie Bojang-Sissoho wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ta ce yanzu haka mahukuntar kasar na tattaunawa da sakatariyar kungiyar ta Commonwealth dake birnin London game da wannan batu.

A shekara ta 2013 ne dai tsohon shugaba Yahya Jammeh ya ayyana ficewar kasar ta Gambia daga kungiyar, yana mai ikirarin cewa, ba za a sake yiwa kasarsa wani mulkin mallaka ba.

Haka kuma a shekarar 2016 tsohuwar gwamnatin Jammeh ta sanarwa MDD shirinta na ficewa daga kasashe mambobin kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya. Sai dai kuma sabon shugaban kasar Adama Barrow ya takawa wannan shiri birki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China