in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya taya murnar bude taron shugabannin kungiyar AU
2016-07-18 09:48:31 cri
A ranar Lahadi, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sako ga masu shirya taron shugabannin kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU karon 27 da ake gudanarwa a Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda, inda ya taya kasashen Afirka da jama'arsu murnar bude taron kolin.

Shugaba Xi ya ce, AU wata tuta ce da ake amfani da ita don hada kan mutanen nahiyar Afirka da kokarin raya nahiyar, wadda take taka muhimmiyar rawa wajen dunkule sassan nahiyar waje guda. Ya ce yana fata kasashen Afirka karkashin jagorancin kungiyar AU, za su dinga samun nasarori a yunkurinsu na neman zaman lafiya da ci gaban kasa.

Haka zalika, shugaban kasar Sin ya nanata cewa, an samu sakamako mai muhimmanci a taron shugabannin dandalin tattaunawar hadin kan kasar Sin da kasashen Afirka, da ya gudana a watan Disamban bara a birnin Johannesburg, inda aka kaddamar da wani sabon mataki ga kokarin bangarorin 2 na hadin gwiwa da neman ci gaba tare. Kasar Sin ta dora muhimmanci matuka ga ci gaban huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, don haka za ta ci gaba da tsayawa kan manufarta ta bin gaskiya, da daukar hakikanan matakai, da kokarin kulla abokantaka, da nuna sahihanci, yayin da take hulda da kasashen Afirka, kuma za ta fi mai da hankali kan adalci maimakon moriya. Za ta kuma aiwatar da manyan shirye-shiryenta guda 10 na hadin gwiwa tare da kasashe Afirka, don kara kyautata huldar dake tsakanin bangarorin 2, tare da amfanawa jama'arsu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China