in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zazzabin Lassa ya halaka mutane 41 a Najeriya
2016-01-13 09:51:08 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, kimanin mutane 41 ne suka gamu da ajalisun cikin mutane 93 da suka kamu da zazzabin Lassa a tarayyar Najeriya.

Ministan lafiya na Najeriya Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a Abuja, fadar mulkin Najeriyar. Ya ce, yanzu haka gwamnatin Najeriyar ta sanar da hukumar lafiya ta duniya WHO game da bullar wannan cuta, kana a nata bangaren, gwamnatin Najeriya tana daukar matakan da suka dace na dakile yaduwar cutar zuwa sauran yankunan karkarar kasar.

A watan da ya gabata ne dai aka samu rahoton bullar cutar a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.

Bayanai na cewa, yanzu haka cutar ta yadu zuwa fiye da jihohin kasar 10, maimakon 12 da ake ta yayatawa. Wannan ita ce, annoba mafi muni da ta barke a kasar cikin shekaru 4 da suka gabata.

An dai fara gano cutar ce a shekarar 1969 a garin Lassa da ke tarayyar Najeriya, kuma cutar tana kama da zazzabin cizon saura na malariya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China