Mr. Luo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin kaddamar da shagulgulan bikin Bazara na wannan shekara da ya gudana a cibiyar yada al'adun kasar Sin dake Madrid,babban birnin kasar Sifaniya,bikin da ya samu halartar ministan ilmi na kasar Sifaniya da takwaransa na al'adu da wasanni Inigo Mendez Vigo.
Ministan wanda ke ziyarar aiki a kasar Sifaniya daga ranar Lahadi zuwa yau Laraba, ya ce,a shekarun baya shagulgulan murnar bikin Bazarar sun samu yabo daga mutane da dama a sassan duniya. Yana kuma fatan, karin jama'a dake kasashen ketare za su kara fahimta tare da jin dadin manufar bikin Bazaran.
Sunan shirin wanda ma'aikatar al'adun kasar Sin ta bullo da shi shi ne "Barka da Bikin Baraza" kuma manufar tsara wadannan shagulgula ita ce, debewa jama'a kewa ta hanyar wadannan shagulgula gami da al'adun Sinawa. (Ibrahim)