Kaza lika kasar ta Sin za ta tsaya kan kokarin aiwatar da shirin "kafuwar kasashe 2" don daidaita batun Falasdinu ta hanyar siyasa, da neman karbar bakuncin wani taron tattaunawa na manyan kusoshi masu rungumar ra'ayin magance rikici, na dukkan bangarorin Fadasdinu da Isra'ila a birnin Beijing na kasar Sin, a shekarar da muke ciki, ta yadda kasar ta Sin za ta kara taka rawar a-zo-a-gani, a yunkurin shawo kan rikicin da ake fama da shi tsakanin bangorin Falasdinu da Isra'ila.
A cewar Song Aiguo, ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi, ya bayyana a kwanakin baya cewa, kasar Sin ta yarda da kudurin da MDD ta zartas kan batutuwan yankin gabas ta tsakiya, musamman ma a fannin matsayin birnin Kudus, don haka take fatan za a daidaita batutuwan bisa tanajin kudurin MDD, wato kafa wata kasa ta Falasdinawa mai cikakken mulkin kai, da kuma 'yancin kanta, bisa iyakar da aka shata a shekarar 1967, tare da mai da gabashin birnin Kudus a matsayin fadar mulkinta.(Bello Wang)