Alkaluman kididdigar sun nuna cewa, karuwar kudin da aka samu a fannin masana'antu ta kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 28000, wadda ta kai kashi 33.9% na kudin kayayyakin da ake fitarwa a kasar wato GDP, jimillar da ta karu da kashi 0.54% bisa dari a shekarar ta bara.
Ban da haka kuma, kudin shiga da kamfanonin kasar Sin suka samu ya fi yawa a shekarar ta 2017, idan an kwatanta da na shekarun da suka gabata, kama daga shekarar 2013.(Bello Wang)