in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara ba da gudummowa ga kara kokarin samun bunkasuwar kasashen duniya tare
2018-01-26 20:19:26 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin za ta kara ba da gudummawa wajen kara azama kan samun bunkasuwar kasashen duniya da raya al'umma mai kyakkyawar makoma.

Madam Hua ta fadi haka ne a yau Jumma'a a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing.

A yau ne kuma aka rufe taron dandalin tattaunawar tattalin arziki a Davos, inda aka tattauna makomar kasar Sin ta fuskar tattalin arziki da gudummawar da Sin take bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.

Dangane da wannan, madam Hua ta ce, kasar Sin na ba da gudummawa ga bunkasuwar duniya a sassa daban daban. Tana samar wa kasashen duniya babbar kasuwa, kyakkyawar damar zuba jari da samun ci gaba. Ban da haka kuma, shawarar "ziri daya da hanya daya" da ta gabatar tana daya daga cikin ayyukan jin dadin jama'a da suka fi samun karbuwa a duniya. Shawarar ta nuna yadda za a kyautata da kuma daidaita al'amuran kasa da kasa, kana ta samar da sabuwar hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China