in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu kula da gandun dajin Saihanba sun samu lambar yabo ta kiyaye muhalli
2017-12-06 08:15:53 cri

Jiya Talata ne, shirin kare muhalli na MDD (UNEP) ya sanar da cewa, masu kula da gandun daji na Saihanba na kasar Sin sun lashe lambar yabo ta kiyaye muhalli ta shekarar 2017, wato lambar yabo mafi daraja a fannin kiyaye muhalli na MDD.

A yammacin jiya ne bisa agogon wurin, hukumar UNEP ta shirya taron manema labaru a yayin babban taron kiyaye muhallin MDD karo na 3 a hedkwatarta dake birnin Nairobin kasar Kenya, inda ta sanar da wadanda suka samu lambar yabo a fannin kiyaye muhalli, ciki har da masu kula da gandun dajin Saihanba, inda suka lashe lambar yabo bisa kokarin alkinta muhalli.

Fadin gandun dajin Saihanba dake arewacin lardin Hebei na kasar Sin, ya kai muraba'in hekta dubu 93. Sakamakon yadda ake sare shi fiye da kima, ya sa ake ta samun yanayin kasar wurin ke lalacewa. A shekarar 1962, mutane fiye da 100 suka soma shuka itatuwa a wurin, bisa wannan kokari ne, yawan fadin gandun dazuka ya karu daga kashi 11.4 cikin dari zuwa kashi 80 cikin dari. Yanzu haka gandun dajin yana samar da tsabtataccen ruwa da ya kai cubik mita miliyan 137 ga biranen Beijing da Tianjin dake dab da shi a yayin da yake samar da iskar da ta kai ton dubu 545 a kowace shekara.

Daraktan hukumar zartaswar UNEP Erik Solheim ya ce, nasarar da aka samu a gandun dajin Saihanba ta nuna cewa, ana iya kyautata muhallin da aka lalata, kana zai taimaka a fannin zuba jari kan batun kyautata muhallin halitu. (Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China