A ranar Laraba ne dai kungiyar za ta bar gida gabanin wasan ta na neman gurbi da za ta buga da Afirka ta kudu ranar Asabar, kamar dai yadda babban kocin kungiyar Christopher Danjuma ya shaidawa manema labarai a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya. Duk kungiyar da ta yi nasara tsakanin kasashen biyu, bayan buga zagaye 2 na wasanni za ta samu daya daga tikiti 2 na buga gasar ta duniya.
Kungiyar ta mata ko Falconets, ta shiga dukkanin gasannin da aka buga ajin na mata 'yan kasa da shekaru 20 tun fara buga gasar a shekarar 2002, wadda a wancan lokacin hukumar FIFA ta sanyawa suna gasar zakarun 'yan kwallo ta mata 'yan kasa da shekaru 19, inda a lokacin duk wacce ta wuce shekaru 19 ba za ta buga gasar ba.
Daga bisani kuma a shekarar 2006 aka kara yawan shekarun zuwa 20. Kana a shekarar 2008 kuma aka mayar da ita gasar cin kofin duniya ta mata.(Saminu Alhassan)