in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a yi bikin nuna wasannin kwamfuta a Zhangzhou
2017-12-20 16:45:39 cri
Shirye shirye sun yi nisa a yanzu haka, na gudanar bikin nuna wasannin da ake yi da na'ura mai kwakwalwa ko kwamfuta, bikin da zai gudana tsakanin ranekun 22 zuwa 24 ga watan nan na Disamba a birnin Zhangzhou, dake kudu maso gabashin kasar Sin.

Yayin bikin za a gudanar da gasanni 3, wadanda suka hada da ESCC na shekarar 2017, da wasan karshe na E-Sports tournament, da kuma E-Sports ecological convention.

Gasar ESCC dai ita ce irin ta ta farko da za a gudanar a matakin kasa, wadda kuma za a gudanar a sabon dakin wasan na'urori masu kwakwalwa da aka gina. An shafe watanni 10 ana zabar 'yan wasan da za su fafata a gasannin 3, kuma tuni aka zabo kungiyoyi 16 daga lardunan kasar 10, wadanda za su kara don lashe kofin kasa a birnin na Zhangzhou.

A cewar mashirya gasar, za a bude dakin wasannin kwamfutar ne kafin babbar gasar dake tafe.

Sabon zauren dai na da fadin sikwaya mita 3,500, yana kuma kunshe da dukkanin ababen da ake bukata domin gudanar da wasannin na'ura mai kwakwalwa, da na gudanar da taruka masu nasaba da hakan. Baya ga wuraren ilmantarwa, da bada horo, da na nune nune.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China