171214-wasan-roller-skating-bello.m4a
|
Musamman ma a wannan lokacin da kasar Sin take kokarin shirin karbar bakuncin wasannin Olympics na lokacin hunturu a shekarar 2020, gwamnatin kasar tana kokarin yayata wasanni masu alaka da kankara tsakanin jama'a. Sa'an nan wasan roller skating, duk da cewa ba wani wasa ne da ake gudanar da shi kan filin kankara ba, amma mun san asalinsa shi ne wasan skating, wani wasan tsere na musamman da ake gudanar da shi kan kankara. Daga bisani don biyan bukatun ci gaba da wasan skating a lokacin da babu kankara, aka kirkiro fasahar sanya wili ko taya a karkashin takalmar skating, wadda ta zamo wasan roller skating ke nan. Saboda haka dukkan fasahohin da ake da su wajen gudanar da wasan roller skating sun yi kama da na wasan skating. Dalilin haka, wasan roller skating ya kara samun damar yaduwa tsakanin al'ummun kasar Sin a wannan lokacin da muke ciki.