in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bulgaria: An bayyana Ivelin Popov a matsayin dan wasa mafi kwarewa a 2017
2018-01-10 16:03:55 cri
Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar kasar Bulgaria, wanda ke wasa a kulaf din Spartak na birnin Moscow Ivelin Popov, ya sake zama dan wasa mafi kwarewa na kasar Bulgaria a bana. Matsayin da ya zamo wa dan wasan na 3 a jere.

Masu kada kuri'a 104 daga kafofin watsa labaran kasar 48 ne suka jefa kuri'ar amincewa da kwazon dan wasan, inda ya samu maki 248, adadin da ya ninka na dan wasan da ya zamo na biyu wato Martin Kamburov.

Dan wasan Botev Plovdiv Todor Nedelev ne kuma ya zamo na 3 da maki 48.

A shekarar da ta gabata, Popov mai shekaru 30 da haihuwa ya kasance cikin 'yan wasan kungiyar sa da suka lashe kofin kalubale na Rasha "Super Cup", ya kuma buga gasar cin kofin zakarun turai tare da kungiyar sa ta Spartak.

A wani ci gaban kuma, Popov, wanda shi ne Kyaftin din kungiyar Bulgaria, ya bada babbar gudun mawa wajen samun nasarar kungiyar kasar sa, a wasan ta da Netherlands inda suka tashi 2 da nema. Da kuma wasan su da Sweden wanda suka tashi 3 da 2, a wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya dake tafe.

Yayin bikin karrama shi, Popov ya ce yana alfahari da wannan nasara da ya cimma. Ya ce yana fatan cin karin kwallaye tare da kungiyar kasar sa.

Cikin shekaru 57 a tarihi, 'yan wasan kasar Dimitar Berbatov, da Hristo Stoichkov ne kadai suka taba kafa irin wannan tarihi na Popov, inda Dimitar Berbatov ya zamo zakaran kasar a fagen taka leda a shekarun 2002, da 2004, da 2005, da 2007, da 2008, da 2009 da kuma 2010.

Shi kuwa Hristo Stoichkov ya rike wannan kambi ne tsakanin shekarun 1989 da 1994. Hristo Bonev ya zamo dakaran kwallon kafar Bulgaria a shekarun 1969, da 1972 da kuma 1973. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China