Souza mai shekaru 32 da haihuwa, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru 2, da dama ta cike shekara ta 3 a Sao Paulo, kan kudi har damar Amurka miliyan 3.6. Souza ya ciwa Recife kwallaye 57 a wasanni 173 da ya buga bayan da ya koma can daga Fluminense a shekarar 2016.
Shafin yanar gizo na kungiyar ta Recife ya bayyana cewa, nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa za a yi wa dan wasan gwaje gwajen lafiya kafin shigar da shi cikin jerin 'yan wasan kungiyar.
Dan wasan ya kuma taba taka leda a Benfica, baya ga kungiyar kasar sa da ya takawa leda a karo 7, an kuma martaba shi cikin manyan 'yan wasan kungiyar, bayan da ya ciwa Brazil din wata kwallo da aka ce ita ce mafiya sauri a tarihin kungiyar. Ya ciwa Brazil kwallon ne cikin watan Yuni, dakika 11 da take wasa tsakanin kasar Brazil din da Australia, wasan da aka buga a Melbourne, aka kuma tashi Brazil din na da kwallaye 4 Australia na nema.(Saminu Alhassan)