Shugaban ya yi jawabi a wajen taron inda ya bayyana cewa, a shekarar 2018 da muke ciki an fara aiwatar da manufofin da aka gabatar a wajen babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, kana wannan shekara ita ce cikar shekaru 40 da aka gabatar da manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar ta Sin, saboda haka ya kasance wani lokaci mai muhimmanci domin gudanar da matakan gyare-gyare a kasar yadda ake bukata. A cewar shugaban, kamata ya yi, a kara kirkiro sabbin fasahohi, da daidaita tunanin mutane, don zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar.
Ban da haka kuma, mahalarta taron sun jaddada cewa, ya kamata a yi kokarin kawar da wasu matsaloli masu alaka da tsare-tsaren kasar a fannoni daban daban, haka kuma a kara yin kwaskwarima ga wasu fannoni musu muhimmanci da suka hada da kamfanonin mallakar gwamnati, da kare ikon mallakar kadarori, harkokin kudi da haraji, da aikin raya yankunan karkara, da aikin kiyaye muhallin halittu, da dai makamantansu.(Bello Wang)