A cikin wasikar, Xi Jinping ya nuna cewa, bayan da aka gudanar da taron ministocin karo na farko a watan Janairu na shekarar 2015, bisa kokarin bangarorin biyu, China-CELAC ya riga ya zama wata muhimmiyar hanya ta hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean, ya kuma sa kaimi ga samun nasarori na hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.
Xi Jinping ya jaddada cewa, a tarihi, Sin da kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean sun bude hanyar siliki a kan tekun Pasifik. A kuma yanzu, bangarorin biyu na tsara sabon shiri bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", a kokarin inganta hadin gwiwarsu da ya ratsa tekun Pasifik, ta yadda za su bude wani sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu. (Zainab)