Shugaban kasar Switzerland, Alain Berset, ya gabatar da jawabi a wajen bikin kaddamar da taron, inda ya ce, akwai sabanin ra'ayi tsakanin kasashe daban-daban a fannonin da suka shafi matsalar sauyin yanayi, yaki da ta'addanci, da kuma wanzar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro. Shekarar da muke ciki, ya kamata ta zama shekara da kasashe suka inganta hadin-gwiwa tsakaninsu.
Alain Berset ya kara da cewa, yayin da duniya ke fuskantar matsaloli da kalubaloli da dama, ya zama dole kowace kasa ta nuna himma da kwazo, da gudanar da harkokin kasuwanci cikin 'yanci, da daga matsayin kowane dan Adam, da kara samar da daidaito tsakanin bil'adama, a wani kokari na samar da aldaci a zamantakewar al'umma.
Yayin taron na yini hudu, za'a gudanar da shawarwari da tattaunawa sama da dari hudu, don malaharta su inganta mu'amala da yin musayar ra'ayoyi gami da habaka hadin-gwiwa tsakaninsu.(Murtala Zhang)