A yayin taron manema labaru da aka shirya a yau a Talata a nan birnin Beijing, darektan zartaswa na dandalin, kuma babban wakilin dandalin dake Sin David Aikman ya bayyana cewa, an shirya taron ne da nufin yin kira ga shugabanni a fannoni daban daban da su gabatar da sabbin shawarwari, tare kuma da daukar hakikanin matakai, don kara imanin al'umma kan makomar bunkasuwar duniya a nan gaba.
Ana saran a yayin taron za a mayar da hankali kan jerin kalubaloli masu tsanani da duniya ke fuskanta a shekarar 2017, ciki har da yadda za a karfafa tsarin hadin kan duniya, don tinkarar tasirin da dunkulewar tattalin arzikin duniya ke haifarwa, da yadda za a sake farfado da tattalin arzikin duniya, don warware matsalolin raguwar saurin ci gaban tattalin arziki da batun matsalar rashin ayyukan yi, kana da yadda za a kawar da matsalar rashin hangen nesa, son kai da cin hanci, don kara kyautatta halin kasuwanni, da kuma yadda za a share fage game da juyin juya halin masana'antu karo na hudu da dai sauransu. (Bilkisu)