Mr. Li ya ce, yanzu, ana shiga wani muhimmin mataki na kara kuzari game da raya tattalin arzikin duniya, kuma tattalin arzikin Sin ya bunkasa yadda ya kamata. A shekarar 2015, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya ci gaba da kasancewa a sahon gaba a duniya, kuma ya zama ginshikin raya tattalin arzikin duniya. Kasar Sin na da kwarewa wajen raya tattalin arziki cikin sauri, kuma za ta bi manufar kirkiro da sabbin abubuwa da daidaita saurin bunkasuwa kuma ba tare da gurbata muhalli ba, da cin gajiyar fasahohin da aka samu, wannan zai taimaka wajen raya tattalin arziki cikin sauri. Kasar Sin kuma za ta ci gaba da bin manufar samar da zaman lafiya da samun bunkasuwa, da hadin gwiwa, da samun moriyar juna tare, don fuskantar kalubale tare da ragowar kasashen duniya.(Bako)