in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanan tattalin arziki sun bukaci a yi taka tsantsan na hasashen tattalin arzikin duniya a taron Davos
2016-01-24 13:35:40 cri
Masanan tatalin arziki da suka hada Christine Lagarde, babbar darektar asusun bada lamuni ta duniya IMF sun yi kiran da a yi taka tsantsan game da tattalin arzikin duniya a wannan shekara dama masu zuwa a gaba.

Madam Lagarde tace ana kallon tattalin arzikin duniyar a shekara ta 2016 zai samu ci gaba amma kuma ba tare da daidaito ba, a jawabin da tayi wajen taron kungiyar masanan tattalin arziki na duniya na Davos, ta kara da cewa akwai tabbaci mai kyau amma akwai kuma hadari a tattare da hakan.

A cigaban da hasashen tattalin arzikin duniyar ya fitar a ranar talatan nan, kungiyar dake da cibiya a birnin Washington ta ce an yi hasashen yawan bunkasuwar tattalin arziki zai kai kashi 3.4% a wannan shekara kuma kashi 3.6% a shekara ta 2017.

Tattalin arzikin duniya na gabatar da gaba daya sauyin yanayin da ke canzawa, amma kuma hadarin dake biye da shi sun hada da saukan farashin kayayyakin masarufi a sanadin saukar kudin mai da tsarin da ya shafi kudade, inji ta a wajen taron da ke da taken hangen tattalin arziki.'

A wani bangaren kuma, sakamakon da aka cimma a taron masanan na cewar kasuwanni sun yi tunanin da ya wuce kima ma Sin. Gyaran tsarin tattalin arzikin Sin dake aukuwa tsakanin masana'antu zuwa samar da hidimomi, daga fitar da kayayyaki ketare zuwa kasuwannin cikin gida da kuma daga zuba jari zuwa sayyaya an yi shi da yawan gaske inji darektar ta IMF.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China