Za a bude dandalin taron tattaunawa na Davos karo na 4 na shekarar 2016, daga ranar 20 zuwa ranar 23 ga wannan wata a garin Davos na kasar Switzerland, kuma babbar ajandar taron na wannan karon shi ne, za'a maida hankali kan batun sauyawar yanayi da ci gaba a sha'anin masana'antu.
Za a tattauna sosai kan yadda sauya fasalin masana'antun a karo na 4 zai inganta yanayin zaman rayuwar bil Adama, da kuma yadda za a tunkari kalubalen da zai iya addabar al'umma. Shugaban babban kamfanin hada-hadar ciniki ta yanar gizo Internet Alibaba Ma Yun da kuma sauran shugabannin kamfannonin yanar gizo za su halarci taron.
Ban da haka kuma, za a tattauna kan batutuwan tsaro da sauyawar yanayi da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da sauransu a yayin taron.(Lami)