Bisa Jadawalin taron, za a gudanar da taron gama gari karo na 35 na wakilan kwamitin dindindin daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Junairu, sannan a gudanar da karo na 32 na taron majalisar zartarwar Tarayyar daga ranar 25 zuwa 26.
Taken taron da zai gudana a hedkwatar Kungiyar dake Addis Ababa shi ne 'nasarar yaki da cin hanci: hanya mai dorewa ta sauya nahiyar Afrika'.
A cewar Tarayyar, taron gama gari na shugabannin kasashen zai gudana daga ranar 28 zuwa 29 ga watan na Junairu. (Fa'iza Mustapha)