in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zanga-zangar da aka yi a Congo Kinshasa ta sa mutane a kalla 5 suka mutu
2018-01-22 10:55:03 cri
An yi babbar zanga-zanga a birnin Kinshasa, fadar mulkin jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, a jiya Lahadi. Inda arangamar da ta barke tsakanin masu zanga-zangar da sojojin gwamnati ta sabbaba rasuwar mutane a kalla 5, yayin da wasu fiye da 10 suka jikkata.

Tawagar wanzar da zaman lafiya da MDD ta girke a Kinshasa ta tabbatar da adadin mutuwar mutanen, kuma ta ce an riga an cafke mutane fiye da 60.

Ana ta samun barkewar zanga-zanga a jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a kwanakin baya, inda masu zanga-zangar ke bukatar gwamnatin kasar da ta gudanar da yarjejeniyar da rukunonin siyasan kasar suka kulla dangane da batun babban zaben kasar.

Wa'adin shugabancin shugaban kasar Joseph Kabila ya riga ya cika tun a watan Disambar shekarar 2016. Amma sakamakon rashin gamsuwar da sassa daban daban na kasar suka nuna dangane da yadda aka jinkirta zaben shugabancin kasar daga shekarar 2016 har zuwa watan Afrilun shekarar 2018, ya sa bangarorin siyasa na kasar suka kulla wata yarjejeniya a farkon shekarar 2017, don kayyade matakan da za a dauka wajen gudanar da babban zabe da kafa sabuwar gwamnati, inda aka tabbatar da cewa gwamnati ba za ta nemi tsawaita wa'adin aikin shugaba Kabila ba, kana za a gudanar da babban zabe a watan Disamban shekarar 2017.

Amma zuwa watan Nuwamban bara, hukumar zabe ta kasar ta sanar da dakatar da gudanar babban zaben har zuwa karshen shekarar 2018, lamarin da ya janyo kin amincewa daga jam'iyyun adawa, wadanda suka tsai da niyyar kaddamar da zanga-zanga don nuna rashin jin dadinsu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China