in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Jamhuriyar Kongo
2017-12-25 11:00:24 cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta yi na'am da yarjejeniyar tsagaita bude wuta wanda aka rattaba hannu kanta tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Kongo da 'yan tawayen kasar karkashin jagorancin Reverend Priest Ntumi.

Shugaban hukumar zartaswar AU, Moussa Faki Mahamat, ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar a karshen makonnin cewa, ya gamsu da yadda aka kulla yarjejeniyar dakatar da tashin hankalin da tsagaita bude wutar tsakanin sassan biyu, wanda aka daddale a Kinkala.

Shugaban ya mika sakon fatan alheri ga dukkan bangarorin, inda yace wannan wani muhimmin mataki ne a kokarin da ake wajen lalibo bakin zaren warware rikicin da ya addabi jamhuriyar Congo.

Sai dai ya gargadi bangarorin da abin ya shafa dasu mutunta yarjejeniyar da aka kulla.

Yace aiwatar da daftarin dake kunshe cikin yarjejniyar zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kuma samar da kyakkyawan yanayin cigaban rayuwar al'ummar Kongo da inganta sha'anin mulkin demokaradiyya a kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China