An soma zanga-zangar ce a ranar 8 ga wata a birnin Tunis, babban birnin kasar, kuma nan da nan ta bazu zuwa larduna fiye da 10 na kasar. Rahotanni na cewa, zanga-zangar ta barke ne sakamakon matsalar kuncin rayuwa da jama'a ke fuskanta, 'yan kasar na fama da tsadar rayuwa, amma dokar kudi ta shekarar 2018 da gwamnatin kasar ta kaddamar ta sa farashin kaya na ci gaba da karuwa.
Firaministan kasar Tunisiya Youssef Chahed ya bayyana cewa, gwamnati ta fahimci bukatun jama'a, amma ba za ta lamunci tashin hankali da zagon kasa ba, kana duk wanda ya karya doka za a hukunta shi. (Bilkisu)