in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin Aljeriya da Tunisiya sun tattauna batun yaki da ta'addanci
2018-01-08 10:43:39 cri
Ministan harkokin cikin gidan kasar Tunisiya, Lotfi Brahem, ya ziyarci kasar Aljeriya a jiya Lahadi, inda ya tattauna tare da jami'in kasar dangane da batun hadin gwiwar kasashensu 2 ta fuskar yaki da ta'addanci.

Wani kamfanin dillancin labaru na kasar Aljeriya ya ruwaito cewa, mista Brahem ya gana da takwaransa na kasar Aljeriya Noureddine Bedoui, daga bisani jami'in na kasar Tunisiya ya gaya wa manema labaru cewa, tun tuni kasashen 2 suka kulla huldar hadin gwiwa a kokarin dakile ta'addanci, amma duk da haka, ya kai ziyara kasar Aljeriya a wannan karo don neman inganta huldar sassan biyu, da habaka ta zuwa sauran ayyuka daban daban.

A nasa bangaren, mista Bedoui na kasar Aljeriya ya ce, tattaunawar da suka yi za ta taimakawa kokarin kyautata musayar ra'ayi tsakanin kasashen 2 a fannonin tsaro da kuma dakile ta'addanci.

An ce kasashen Aljeriya da Tunisiya a shekarun baya bayan nan, na kara yin hadin kai tsakaninsu game da ayyukan samar da bayanai, da kuma daukar matakan soja, tare da gudanar da wasu atisayen soja a yankin kan iyakar dake tsakaninsu, don magance shigar 'yan ta'adda zuwa yankunan Maghreb da Sahel ta kasashen biyu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China