Wata majiyar jami'an tsaron kasar data nemi a sakaye sunanta ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an damke wasu mayakan 4 da ransu.
Wasu kwarrarrun bangarori na jami'an tsaron kasar ne suka kaddamar da simamen, cikinsu har da wata rundunar tsaron kasar ta musamman, wacce ta shafe makonni masu yawa tana farautar mayakan.
Youssef Chahed ya sanar a cibiyar horas da jami'an tsaron kasar dake Bir Bouregba mai tazarar kilomita 60 daga Tunis babban birnin kasar cewa, bayan gudanar da bincike da jami'an tsaron suka yi cikin makonnin da suka wuce, sun yi nasarar gano maboyar 'yan bindigar inda daga bisani suka yi musu dirar mikiya suka hallaka biyu daga cikinsu kana suka kama wasu da ransu.
A cewar Chahed, 'yan kungiyar masu tsattsaunaran ra'ayin addini sun yi yunkurin kaddamar da hare haren ta'addanci a kasar ne a lokacin watan Ramada mai tsarki dake tafe.(Ahmad Fagam)