in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Tunisiya sun kama wasu masu tsattsauran ra'ayi uku
2016-12-25 13:19:27 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya a jiya Asabar ta sanar da cewa, an kama wasu masu tsattsauran ra'ayi uku da ke da hannun kai hari kasuwar Kirismeti ta birnin Berlin a kasar Jamus.

Wata sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya ta fitar ta yi nuni da cewa, wadannan mutane uku masu shekaru 18 zuwa 27 da haihuwa suna karkashin wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini, kuma daya daga cikinsu dangi ne na dan kasar Tunisiya Anis Amri, wanda ya kai harin.

Sanarwar ta ce, sashen leken asiri na rundunar tsaron Tunisiya sun samu labarin mutanen nan, har ma an bi su an kama su.

A labarin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Tunisiya ta bayar, an ce, wani daga cikin mutanen uku ya amince da tuntubar Anis Amri ta wani manhaja na waya, don gudu daga sa ido na sassan tsaro, mutumin nan ya kuma yi shelar mara wa kungiyar IS baya.

A ranar 19 ga wata da dare, Anis Amri ya tuki wata babbar mota wadda ta kauce ta shiga cikin taron jama'a da ke sayayya a kasuwar kirsimati a birnin Berlin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu kusan 50. 'Yan sandan kasar Italiya sun harbe Anis a ranar 23 ga wata a birnin Milan.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China