in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Muna da sunayen 'yan ta'adda fiye da 2900' in ji gwamnatin Tunisiya
2017-01-04 11:01:10 cri
Jiya Talata, ministan harkokin cikin gidan kasar Tunisiya Hedi Majdoub ya ce, hukumar tsaron kasar na da jerin sunayen wasu 'yan ta'adda 'yan asalin kasar sama da 2900, ciki har da kimanin mutane 300 mafiya hadari.

Yayin da ya zanta da Jaridar Le Maghreb ta kasar, Hedi Majdoub, yana mai cewa, hukumar tsaron kasar ta ayyana mutane 2929 a matsayin 'yan ta'adda, ciki har da fiye da 1000 a kasar Siriya, wasu 500 suna Libiya, kusan 150 kuma suna kasar ta Iraki.

Bugu da kari, akwai kimanin 'yan ta'adda su 400 wadanda ba'a san inda suke ba. 'Watakila suna yankunan dake fama da rikici, ko kasashen Turai', a cewar Hedi Majdoub. A halin yanzu, hukumar leken asirin Tunisiya na kokarin hada kai tare da sauran wasu kasashe, domin tabbatar da inda wadannan 'yan ta'adda suke.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China