Cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan fara ziyarar aiki ne a nahiyar Afirka ce. Game da wannan batu, Lu Kang ya bayyana cewa, inganta hadin kai da hadin gwiwa tare da kasashen Afirka muhimmin tushe ne na manufofin diplomasiyyar kasar Sin. A cikin shekaru fiye da 20 da suka gabata, ministocin harkokin wajen kasar Sin su kan fara ziyararsu ta farko cikin sabuwar shekara a nahiyar Afirka, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi yana ci gaba da wannan al'ada, matakin da ya bayyana cewa, Sin na dora muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka. A wannan ziyara, za a karfafa mu'amala tare da nahiyar Afirka, tare da sa kaimi ga aiwatar da daidaiton da shugaban kasar Sin ya cimma tare da shugabannin kasashen Afirka, sa'an nan, za a kara yin imani da juna a fannin siyasa da zurfafa hadin gwiwarsu, tare kuma da share fagen taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da za a gudanar a kasar Sin a bana. (Zainab)




