in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Asiya da Turai karo na 13
2017-11-21 11:11:13 cri

A jiya Litinin ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen Asiya da Turai karo na 13 da aka gudanar a birnin Naypyitaw,babban birnin kasar Myanmar, inda ya yi jawabi mai taken "raya sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Asiya da Turai a sabon zamani".

Wang Yi ya bayyana cewa, taron a tsakanin Asiya da Turai wata sabuwar hanya ce ta yin mu'amala a tsakanin kasashen duniya, inda za a yi shawarwari da hadin gwiwa a maimakon rashin nuna kiyayya da juna, inda za a sada zumunta a maimakon kulla kawance, hakan shi ne zai tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Bangarorin biyu sun himmatu ga raya tattalin arziki a duniya bisa tsarin bai daya, da fadada yin ciniki da zuba jari, hakan zai taimaka ga samun ci gaba a nahiyar Asiya da Turai. Ya kara da dewa, kamata ya yi a yi la'akari da kasancewar nau'o'in al'adu daban daban a Asiya da Turai, da yin mu'amala da juna, da sada zumunta a tsakanin jama'arsu. Kana a yi tunanin raya bangarori daban daban, da sa kaimi ga kyautata da yin kwaskwarima kan tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa ta yadda za a hada kai wajen tinkarar kalubale tare.

Game da makomar hadin gwiwar Asiya da Turai, Wang Yi ya gabatar da shawarwari guda uku. Na farko, ya kamata a hada kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A nuna goyon baya ga kasashen yankin ta yadda za su warware matsala ta hanyar yin shawarwari kai tsaye, kana sauran bangarori su ba da gudummawa da gudanar da aiki bisa ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Na biyu, ya kamata a bullo da sabon fanni na samun ci gaba. A nuna goyon baya ga tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban, da kin amincewa da duk wani irin ra'ayin bada kariya ga ciniki, da karfafa matakan saukaka harkokin ciniki da zuba jari cikin 'yanci, da a yi kokarin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin duniya bisa tsarin bude kofa da samun moriyar juna, da kuma daidaito. Na uku, a yi kokarin gano tsarin tafiyar da harkokin duniya mai dorewa. Ya ce wasu kasashe sun samu kwarewa a fannonin kawar da talauci, yaki da gurbacewar muhalli, yaki da cin hanci da rashawa, a don haka taron da ake gudanarwa a tsakanin Asiya da Turai zai iya zamanto wani muhimmin dandali na yin musayar fasahohi da warware matsalolin bunkasuwa tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China