in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana dab sanar da sabbin ministocin kasar Birtaniya
2018-01-08 13:26:45 cri
Firaministar kasar Birtaniya Theresa May, za ta sanar da sunayen wasu sabbin ministocin kasar a yau Litinin, kamar yadda wasu kafofin watsa labaru na kasar suka bayyana a jiya Lahadi.

An ce dalilin da ya sa Madam May take neman sauya wasu ministoci shi ne domin tana son shigar da wasu mata da wadanda ba fararen fata ba cikin majalissar ministocin, ta yadda za ta samu damar samun karin kuri'u a babban zaben kasar karo mai zuwa.

Ban da haka, a wannan karo Theresa May za ta sanar da sunan sabon babban ministan kasar, wato mataimakinta cikin majalisar monistoci. An ce akwai yiwuwa za a danka wa ministan lafiya na yanzu Jeremy Hunt wannan mukami.

Tsohon babban ministan kasar Damian Green ya yi murabus a watan jiya, sakamakon yadda ake zarginsa da yin faduwar toto a ruwa.

Sauran bayanan da kafofin watsa labarun kasar suka gabatar sun nuna cewa, za a sauya ministoci masu kula da ayyukan ilimi, da kasuwanci, da masana'antu, da dai sauransu. Yayin da ministoci masu kula da harkar diplomasiyya, da aikin kudi, da harkokin cikin gida, ba za a canza su ba.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China