in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PM: Babu canji game da ziyarar Trump zuwa Birtaniya
2017-06-12 10:05:45 cri
Mai magana da yawun ofishin firaiministar Birtaniya ya sanar cewa, babu sauyi game da batun ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump zai kai kasar Birtaniyan, bayan da jaridar Guardian ta bada rahoton yiwuwar soke wannan ziyara.

Jaridar ta Guardian dai ta ruwaito cewa, Trump ya fadawa firaiministar Birtaniya Theresa May ta wayar tarho cewa, ba zai samu damar ziyarar aiki da ya shirya kaiwa Birtaniyan ba har sai al'ummar kasar sun nuna goyon bayansu game da wannan ziyara, a lokacin tattaunawar, mashawarci ga fadar mulkin Birtaniyan yana dakin a lokaci hirar tasu.

Kakakin fadar ta Downing Street ya bayyana cewar, ba za su yi karin haske game da wannan jita-jitar da ake bazawa ba, wannan ya shafi tattaunawar sirri ne tsakanin shugabannin biyu.

A wani sakon e-mail wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bi diddiginsa ya nuna cewa, sarauniyar Ingila ta tsawaita takardar gayyatar da aka yiwa Mista Trump zuwa Birtaniyan, kuma babu sauyi game da wanan shiri.

Theresa May ta gayyaci shugaba Trump zuwa Birtaniyan ne kwanaki 7 bayan ya sha rantsuwar kama aiki, yayin da May din ta kasance shugaba ta farko daga kasar waje da ta ziyarce a fadar ta White House. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China