in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministar Birtaniya ta nada sabon ministan harkokin tsaron kasar
2017-11-03 11:09:36 cri
Firaministar kasar Birtaniya Theresa May, ta nada jami'in kula da ladabtarwa na jam'iyyar Conservative ta kasar Birtaniya, Gavin Williamson, a matsayin sabon ministan harkokin tsaron kasar, don ya maye gurbin tsohon ministan tsaron kasar Michael Fallon, wanda ya yi murabus ba zato ba tsammani a ranar 1 ga wannan wata.

An haifi Williamson a shekarar 1976, wanda ya taba zama mai ba da taimako ga tsohon firaministan kasar Birtaniya David Cameron a gun majalisar dokokin kasar, bayan da Theresa May ta zama firaministar kasar a watan Yuli na shekarar 2016, ya zama babban jami'in kula da ladabtarwa na jam'iyyar Conservative ta kasar.

Kafar yada labarai ta BBC ta bayar da labari cewa, Williamson bai taba shiga aikin soja ba, kana bai tsufa ba, sannan fadar firaministar kasar ta yi imani da shi a dogon lokaci.

A ranar 1 ga wannan wata, Michael Fallon, wanda ya zama ministan tsaron kasar Birtaniya har na tsawon shekaru 3 ya sanar da yin murabus, shi ne memba na farko na gwamnatin kasar Birtaniya a wannan karo da ya yi murabus. A cikin wasikar, bai bayyana dalilin yin murabus din nasa ba, ya ce wasu ayyukan da yake gudanarwa ba su dace da zaton jama'a da aka yiwa bangaren soja na kasar ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China