Cikin wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar a jiya, sun ce an kama mutumin mai shekaru 18 a duniya bisa zargin aikata ayyukan ta'addanci.
A nasa bangaren, babban jami'in 'yan sandan birnin London, ya ce aikin da aka gudanar na cafke mutumin na da muhimmanci matuka, sannan za a kiyaye matsayin koli na barazanar harin ta'addancin da kasar ke fuskanta, wato mataki mafi hadari.
A ranar Jumma'a da ta gabata ne, aka samu fashewar bom a wata tashar jirgin karkashin kasa a yammacin birnin London, lamarin da ya haddasa jikkatar mutane kimanin 30.
Daga bisani dai, kungiyar IS mai kaifin kishin Islama ta sanar da daukar nauyin harin.
Zuwa daren Jumma'ar ne kuma, firaministar Birtaniya Teresa May ta sanar da daga matsayin barazanar ta'addancin da kasar ke fuskanta, daga matsayi 'mai tsanani' zuwa 'mafi hadari'.(Bello Wang)