A yayin taron, Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta gabatar da batun yaki da cin hanci da rashawa, da kudurin ta na cafke 'yan kasar ta da suka aikata laifin cin hanci ko al'mundahanar kudade. Matakin da ya samu goyon baya daga hadaddiyar daular Larabawa.
Mr. Wang ya kara da cewa, kasashen biyu na hadin gwiwa wajen aikin mika mutanen da suka aikata laifi a kasar Sin, kana ya yi imanin cewa, hadaddiyar daular Larabawa, ba za ta zama mafaka ga wadanda suka aikata cin hanci a kasar Sin ba. (Zainab)