in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaiministan Sin ya nanata aniyar gwamnati wajen yaki da rashawa
2017-04-10 09:40:51 cri
Firaiministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada aniyar gwamnatin kasar wajen tsabtace harkokikin mulki, tare da bibiyar yadda ake tafiyar da harkokin kudaden gwamnati domin tsananta shirin yaki da rashawa a sha'anin mulki a kasar.

Li, ya bayyana cewa, kasar Sin ta cimma manyan nasarori a shirinta na tsabtace gwamnati da kuma yaki da rashawa a shekarar 2016, sai dai a cewarsa, har yanzu akwai sauran matsaloli wadanda suke bukatar daukar tsauraran matakai, kamar yadda aka rawaito cikin jawabin da mista Li ya gabatar a ranar 21 ga watan Maris game da tsabtace gwamnati, wanda aka fitar da jawabin a jiya Lahadi.

Firaiministan na Sin ya ce dukiyar gwamnati mallaki ne na dukkan jama'ar kasa, kuma da ita ce ake gina tattalin arzikin kasa, a don haka, ya bukaci dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati su dauki tsauraran matakai wajen hana zirarewar dukiyar gwamnati, kuma su samar da kanda-garkin yaki na cin hanci a sha'anin kudade.

A shekarar 2016, hukumomin dake kula da da'a na kasar Sin, sun hukunta mutane dubu 415 wadanda aka samu da hannu wajen saba dokokin aiki, kana wasu 'yan kasar sama da dubu daya ne da suka tsere zuwa kasashen waje aka tusa keyarsa suka dawo kasar ta Sin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China