Milad Saadi, jami'in watsa labarai na ofishin yaki da kwararar bakin haure a Tripoli ya bayyana cewa, a cikin wannan shekarar kasar Libyan ta tusa keyar bakin haure da yawansu ya kai 13,000 zuwa kasashensu na asali, ta hanyar hadin gwiwa da hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa IOM.
A shekarar 2006, IOM da hukumomin kasar ta Libya, sun kaddamar da wani shiri na kwashe bakin hauren dake gararamba a kasar Libyan don mayar da su kasashensu na asali.
Saadi ya ce, mafi yawan kasashen larabawa dana Afrika, suna aiki tare da sashen kula da bakin hauren don tabbatar da ganin an mayar da 'yan kasashen nasu gida.
Ya ce a kwanan nan kasar Morocco ta fara hada kai da sashen ta hanyar tura wakilai na musamman daga Rabat. Ana sa ran bakin haure 'yan kasar Morocco 265 ne za'a kwashe su a karshen wannan mako.(Ahmad Fagam)