in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta kafa cibiyar bincike a kusa da Sirte na kasar Libya
2017-12-21 10:22:41 cri
Mayakan kungiya mai da'awar kafa daular Musulunci (IS) ta kafa wata cibiyar binciken ababen hawa a kusa da garin Jurfa na kasar Libya, wanda ya kasance kusa da yankin Sirte wajen da a baya ya taba zama babban sansanin mayakan na IS, inda suke binciken sojoji da jami'an tsaro.

Wata majiyar jami'an tsaro ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, IS ta kafa cibiyar binciken ne a kan hanyar zuwa Jurfa dake kusa da Sirte. Sai dai suna yawan sauya wajen binciken.

Majiyar ta kara da cewa, fararen hula dake wucewa ta hanyar sun tabbatar da cewa a ranar Laraba mayakan na IS sun tsayar da su. Akwai motoci 3 dauke da makamai na mayakan 'yan ta'addan a gefen hanyoyin. Suna bincika motocin dake dauke da fararen hular domin tantancesu, suna neman sojoji ne ko kuma jami'an tsaro.

Mayakan suna amfani da damar yanayin sanyi ne inda suke yin binciken cikin gaggawa, sai dai babu jami'an tsaro masu yawa dake aikin sintiri a daidai wannan lokacin, inji majiyar.

A watan Disambar shekarar 2015, dakarun tsaron gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD suka fatattaki mayakan na IS daga yankin Sirte, mai nisan kilomita 450 daga gabashin birnin Tripoli. Daga nan ne mayakan na IS suka fantsama zuwa yankin kudancin kasar da kuma yankunan dake da tsaunuka.

Sai dai daga lokaci zuwa lokaci mayakan 'yan ta'addan suna kafa cibiyoyin bincike na tafi da gidanka a kan hanyar data ratsa biranen kudancin kasar Libyan, inda suke bincika motocin dake dauke da farafen hula don zakulo sojoji ko kuma jami'an tsaro don yin garkuwa da su, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China