in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar koli ta kasar Libya ta bukaci a mayar da hankali kan warware dambarwar siyasa
2017-12-21 10:30:40 cri
Majalisar kolin kasar Libya dake zaune a birnin Tripoli ta bukaci majalsiar dokokin kasar dake gabashin kasar data amince da shirin yarjejeniyar zaman lafiyar kasar wanda MDD ta dauki nauyin tsarawa.

Aburrahman Swehli, shugabann majalisar kolin, shi ne yayi kiran a lokacin ganawa da jakadan Birtaniya a kasar Libya, Peter Millett.

A cewar ofishin yada labaran majalisar kolin, a lokacin ganawar tasu sun tattauna batun cigaban da aka samu game da tattaunawa kan rikicin siyasar kasar da kuma kudurin da MDD ta tsara game da shirin zaman lafiyar kasar ta Libya.

A sanarwar da majalisar kolin kasar Libyan ta fitar, Swehli, ya bukaci majalisar dokokin dake gabashin kasar data bayyana matsayarta game da batun tattaunawar warware dambarwar siyasar kasar, kuma ta amince da kudurin tabbatar da zaman lafiyar kasar kafin a kai ga mataki na gaba.

Sanarwar ta kara da cewa, Swehli ya nanata muhimmancin amincewar dukkan bangarorin siyasar kasar, ciki har da majalisar wakilan kasar, a kan yunkurin warware rikicin siyasar kasar.

Sannan ya bayyana aniyar majalisar kolin kasar wajen goyon bayan amfani da matakan siyasa ta hanyar cimma daidaito, da hadin gwiwa, da yin watsi da matakin da tsagi guda na majalisar ya zartas bisa radin kansa.

Swehli, ya buga misali da yunkurin nada sabon gwamnan babban bankin kasar da aka yi wanda ya ce matakin ya saba da dokokin yarjejeniyar sulhu na cikin gida da na kasa da kasa.

Kasar Libya tana fama da matsalar rarrabuwar kawuna ne tsakanin gwamnatin dake gabashi dake zaune a Tobruk, da kuma gwamnatin dake yammaci dake zaune a Tripoli, wadanda suka kafa bankunan tsakiyar kasar biyu.

Duk da kasancewar jam'iyyun siyasar Libyan sun sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da MDD ke jagoranta da nufin kawo karshen rabuwar kawuna a kasar. Sai dai har yanzu kasar Libyan ta kasance a rarrabe ta fuskar siyasa a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tabarbarewar tsaro da rikice-rikice.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China