in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin don murnar sabuwar shekarar ta 2018
2017-12-31 19:00:07 cri

A halin yanzu, ana nuna kyakkyawan fata kan makomar dan Adam ta fuskar zaman lafiya da bunkasuwa, yayin da wasu suke nuna damuwa. Dukkansu suna fatan kasar Sin zata bayyana matsayinta da ra'ayinta a bayyane kuma a fili. Dukkan 'yan Adam na kasancewa kamar wani babban iyali ne. A matsayinmu na wata babbar kasa wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, kasar Sin tana da nata ra'ayi. Kasar Sin tana tsayawa kan kiyaye marbatar MDD da matsayinta. Tana kuma nuna kwazo wajen sauke nauyinta a al'amurran kasa da kasa. Tana cika alkawarinta dangane da daidaita sauyin yanayi a duniya. Sannan tana kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Tun a da can da har zuwa yanzu, kasar Sin tana himmantuwa wajen shimfida zaman lafiya a duniya, tana ba da gudummawa wajen raya duniya, tana kuma kiyaye oda da tsarin kasa da kasa. Jama'ar kasar ta Sin suna son hada kai da jama'ar kasa da kasa wajen samun makoma mai wadata da kwanciyar hankali.

Abokan aiki da abokan arziki, maza da mata: 

Jama'a ne ke kokarin kirkiro babban ci gaban da muka samu. Don haka dole ne jama'ar kasar su ci gajiyar nasarorin. Na gane cewa, jama'armu sun fi mai da hankali kan samun ilmi, da aikin yi, da kudin shiga, da inshorar zaman al'umma, da kiwon lafiya, da kulawa da tsoffi, da samun wurin kwana, da yanayin duniyarmu da dai sauransu. Wasu suna jin dadin zamansu, yayin da wasu suke nuna damuwa, ba su ji dadi sosai. Muna bukatar ci gaba da kokarinmu a wasu ayyukan jin dadin jama'a, hakan da ya bukace mu kara sauke nauyin dake bisa wuyanmu, mu gudanar da ayyukan jin dadin jama'a yadda ya kamata. Har ila yau tilas ne kwamitocin JKS a matakai daban daban, hukumomin wurare daban daban da jami'ai su mayar da moriyar fararen hula a cikin zukatansu a kullum. Wajibi ne su mayar da kawo wa jama'a alheri a matsayin aikinsu mafi muhimmanci, su warware dukkan matsalolin da jama'a suke fuskanta, su fitar da su daga wahalar da suka sha, a kokarin ganin jama'ar Sin sun kara jin dadin zamansu.

Na gode!


1  2  3  4  5  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China