in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin don murnar sabuwar shekarar ta 2018
2017-12-31 19:00:07 cri

Kasar Sin ta kuma samu nasarori da dama a fannonin kimiyya da fasaha, yin kirkire-kirkire, da manyan ayyuka. Tauraron dan Adam na Huiyan yana zagayawa cikin sararin samaniya. An samu nasarar yin gwajin babban jirgin sama kirar C919. Sannan an samu nasarar fitar da na'ura mai kwakwalwa ta zamani. An kammala gwajin shuka shinkafa a cikin ruwan teku. An soma gwajin babban jirgin ruwan yaki mai dauke da jiragen saman yaki cikin ruwa. Injin bincike na musamman mai suna Haiyi ya kammala aikin binciken cikin ruwan teku mai matukar zurfi. A karo na farko kasar Sin ta hako wani nau'in kankarar da ake iya konawa. Tashar jiragen ruwa ta Yangshan da take sarrafa kanta ta bude kofarta. An gama gina babbar gada data hade Hong Kong, da Zhuhai da Macao baki daya. Jirgin kasa mai saurin tafiya kirar Fuxing ya fara tafiya a duk fadin kasar ta Sin. Ina jinjinawa da kuma yabawa kwarewar jama'ar Sin ta yin kirkire-kirkire!

A sansanin soja na yin rawar daji na Zhurihe, mun gudanar da atisayen soja domin tunawa da cika shekaru 90 da kafuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin PLA. A yayin da aka cika shekaru 20 da komowar Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin, na kai ziyara a Hong Kong. Na ganewa a idona cewa, sakamakon cikakken goyon baya daga gwamnatin tsakiyar kasar, Hong Kong ta ci gaba da samun dadaddiyar wadata da kwanciyar hankali. Tabbas ne Hong Kong zata kara samun makoma mai kyau! Har ila yau, mun gudanar da taron tunawa da cika shekaru 80 da kaddamar da yaki da mahara Japanawa, da taron tunawa da wadanda suka rasa rayukansu cikin kisan kiyashi da mahara Japanawa suka yi a birnin Nanjing na kasar Sin, a kokarin tunawa da tarihi da nuna fatan samun zaman lafiya nan gaba.

1  2  3  4  5  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China