in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin shugaba Xi Jinping na kasar Sin don murnar sabuwar shekarar ta 2018
2017-12-31 19:00:07 cri

Haka zalika, mun shirya wasu tarurrukan diplomasiyya a nan kasar Sin, kamar taron dandalin tattaunawa na koli kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", taron shugabannin kasashen BRICS na Xiamen, da taron tattaunawa tsakanin kusoshin JKS da na jam'iyyun siyasa na kasa da kasa. Ban da haka kuma, na halarci wasu muhimman tarurrukan kasa da kasa. A farkon wannan shekara, na halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya na Davos. Sannan na yi jawabi a babban zauren MDD dake birnin Geneva. Bugu da kari na halarci taron koli na kasashe mambobin kungiyar G20, da kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar APEC. A yayin wadannan tarurruka, na yi musayar ra'ayoyi da sassa daban daban masu ruwa da tsaki, wadanda suka amince da kara azama kan raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama, a kokarin kawo wa al'ummomin kasa da kasa alheri.

A shekarar 2017, na samu wasiku masu yawa daga al'ummar kasar, kamar wadanda suke zaune a garin Yumai da ke gundumar Longzi a jihar Xizang, da makiyayya daga yankin Suniteyou a jihar Mongolia ta Gida, da kuma shehun malami wanda ya taba shiga aikin kaurar da jami'a ta Xi'an zuwa yammacin kasar a shekaru 1950. Sannan akwai wasikar dana samu daga daliban jami'ar Nankai wadanda suka zama sabbin sojoji. Labarunsu sun burge ni matuka. Al'ummomin Sinawa na tsayawa kan kishin kasa, bautawa kasarmu ba tare da yin da-na-sani ba. A ganina, al'mmomin fararen hula, su ne manyan mutane. Kana kuma, ba za a iya jin dadin zaman rayuwa ba, dole sai an yi iyakacin kokarin yin aiki.

1  2  3  4  5  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China